Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 12 a Kano

0
6

Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 12 a Kano

Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a safiyar Juma’a a ƙauyen Samawa, dake karamar hukumar Garun Malam, a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta ƙasa (FRSC) reshen Kano, CC MB Bature, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 2:40 na dare, inda ya haɗa da tirela kirar DAF CF95 mai lambar rajista KMC 931 ZE.

A cewarsa, tirelar tana ɗauke da kaya da suka haɗa da kayan yaji na Ajinomoto da kuma fasinjoji, sai ta samu matsalar na’ura lokacin da “ƙugun gaban tirela ya tsinke,” wanda ya raba kan tirelar daga jikinta, ya sa direban ya rasa ikon tafiyar da ita.

Daga cikin mutane 19 da ke cikin motar, 12 sun mutu nan take, biyar sun ji rauni, yayin da biyu suka tsira ba tare da rauni ba. An garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa Asibitin Kura, yayin da aka ajiye gawarwakin a Asibitin Nassarawa.

Bature ya bayyana cewa haɗa fasinjoji, kaya, da dabbobi a mota guda na jefa rayukan mutane cikin haɗari. Ya kuma yi kira ga direbobi su bi ƙa’idojin hanya sosai, in ba haka ba su fuskanci hukunci mai tsanani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here