Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan ƙasar China a matsayin mai bashi shawara a fannin tattalin arziki

0
19

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya naɗa ɗan ƙasar China, Mr. Li Zhensheng, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Bauchi da Cibiyar Binciken Haɗin Gwiwar Ci gaban China a Bauchi.

Gwamnan ya ce haɗin gwiwar na da nufin mayar da Bauchi cibiyar hulɗa da ƙasashen duniya tare da hanzarta zuba jari da ci gaba a fannoni kamar noma, ilimi, kiwon lafiya, sarrafa masana’antu, hakar ma’adinai, mai da iskar gas, da sauƙaƙe harkokin kasuwanci.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, jihar Bauchi za ta kafa ofishin wakilan ta a China domin kula da ayyuka tare da tabbatar da an kammala su akan lokaci. Wannan haɗin gwiwa, in ji gwamnan, na da alaka da ƙarin ƙarfafa dangantaka tsakanin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Shugaban China Xi Jinping.

Mr. Li, wanda kuma shi ne shugaban Cibiyar Binciken Haɗin Gwiwar Ci gaban China, ya tabbatar da aniyarsu ta tallafa wa Bauchi wajen bunƙasa tattalin arziki ta hanyar ci gaba mai ɗorewa, inganta ababen more rayuwa, da ingancin rayuwar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here