Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bayar da bashi har naira miliyan 10 ga ma’aikatan jami’o’i, kwalejojin ilimi da na kimiyya domin sayen ababen hawa, jarin noma ko ci gaba da karatu.
Sai dai ƙungiyoyin ma’aikata, ciki har da ASUU, sun yi watsi da shirin, suna cewa bai kamata a bayar da bashi ba alhali gwamnati ba ta biya musu haƙƙoƙin da suke bin ta ba tun 2009.
Shugaban ASUU na BUK, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj, ya ce kamata ya yi gwamnati ta fara biyan albashi da alawus, ta kuma sabunta yarjejeniyar 2009 kafin batun bashi.
Duk da haka, ma’aikatar ilimi ta ce shirin zai inganta rayuwar ma’aikata, kuma za a biya cikin shekaru biyar.