APC da PDP kungiyoyin ƴan ta’adda ne—Kotun Canada

0
22

Kotun Tarayya a ƙasar Canada ta hana wani tsohon ɗan siyasar Najeriya, Douglas Egharevba, samun mafaka, tare da bayyana manyan jam’iyyun siyasa na APC da PDP, a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci.

Hukuncin, wanda alkali Phuong Ngo ya yanke a ranar 17 ga Yuni 2025, ya ce akwai ’yan siyasa daga PDP ciki har da manyan jiga-jigai da suka aikata ko suka yi shiru kan laifukan siyasa, abin da ya nuna alaƙa tsakanin shugabancin jam’iyyun da ayyukan ta’addanci.

Jaridar Peoples Gazette ta ruwaito cewa wannan matakin ya tayar da ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda ake jiran gwamnatin tarayya ta bayyana matsayinta. Wani babban jami’in gwamnati ya bayyana cewa hukuncin abin takaici ne, amma sai an tabbatar da sahihancinsa kafin a yi martani.

PDP, ta bakin mambanta a kwamitin zartarwa, Timothy Osadolor, ta ce hukuncin ya dogara ne kan ra’ayin kotu ba tare da hujja mai ƙarfi ba. Ta ce kamata ya yi a bayyana sunayen mutanen da ke da hannu a ta’addanci, musamman a APC, maimakon a ɗaure jam’iyya gaba ɗaya.

Ƙoƙarin jin ta bakin APC da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya bai yi nasara ba, in ji rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here