Rundunar Sojin ƙasar nan ta tabbatar da afkuwar wata ƙaramar fashewa da ta haifar da gobara a barikin Ilese da ke Ijebu-Ode, Jihar Ogun, da safiyar Alhamis.
Daraktan yaɗa labaran rundunar, Laftanar Kanal Apolonia Anele, ya bayyana lamarin a matsayin ƙaramin abu, tare da tabbatar wa jama’a cewa babu abin damuwa a fashewar.
A cewar sanarwar: “Da safiyar yau, 14 ga Agusta 2025, an samu fashewa a cikin ɗaya daga cikin ɗakunan ajiya na rundunar 42, wanda ya haddasa ƙaramar gobara. Da gaggawa sojoji tare da haɗin gwiwar hukumar kashe gobara ta Ijebu-Ode suka shawo kan wutar.
“Muhimmin abu shi ne, babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni. Lalacewar ta tsaya ne kawai a ginin da abin ya shafa da kuma wasu kayayyakin da aka adana. Ana ci gaba da bincike don tantance adadin asarar kayan, inji shi.
Rundunar sojin ta yi kira ga mazauna Ilese da ƙauyukan da ke kewaye da su da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, domin bincike mai zurfi yana gudana tare da sauran hukumomi don gano musabbabin lamarin da kuma kauce wa maimaituwar sa.