Yan bindiga sun kai wa Malamin Islama da matarsa hari a Kano

0
10
Kano

Wani malamin addinin Musulunci, Malam Kabir Idris, da matarsa sun jikkata sosai bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai musu farmaki a gidansu da ke unguwar Danrimi, Rijiyar Lemo, a karamar hukumar Fagge, a daren Talata.

Malam Idris, wanda shi ne shugaban Madrasatul Kanzul Huda, ya bayyana cewa maharan sun shigo gidan sa yayin da yake barci, ba tare da satar waya ko babur da ke wajen gida ba. Ya ce, maimakon haka, sun yi musu barazana sannan suka kai musu hari da adda.

Idris ya samu raunuka guda shida a hannunsa da kuma guda biyu a kansa, yayin da matarsa ta samu raunuka biyu a hannunta.

Kungiyar Malaman Makarantun Addinin Musulunci ta Jihar Kano ta yi tir da wannan mummunan hari tare da kira ga hukumomin tsaro su binciki lamarin.

Yanzu haka Malam Idris na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Murtala, sai dai an jinkirta yi masa tiyata saboda ƙarancin kuɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here