Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Louis Odion a matsayin Kwamishinan Ayyuka, da Ummasalma Isiyaku Rabiu a matsayin Kwamishinar Harkokin Gudanarwa a Hukumar Kula da Gasa da Kare Hakkin Masu Siyan Kaya ta ƙasa (FCCPC).
Sanarwar da Mai Bawa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce majalisar dattawa za ta tantance su kafin amincewa da naɗin kamar yadda dokar FCCPC ta 2018, ta tanada.
Louis Odion, ɗan asalin jihar Edo, gogaggen ɗan jarida ne kuma tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo. Ya taba rike mukamin Kwamishinan Yaɗa Labarai a jihar Edo.
Ummasalma Rabiu, ‘yar shekara 35 daga Kano, ita ce ta kafa Usir Foundation, ƙungiyar agaji da ke taimaka wa marasa galihu ta hanyar ilimi, koyon sana’o’i, da shirye-shiryen jin ƙai. Ta kammala karatu a fannin gudanarwar kasuwanci, kuma shahararriyar ‘yar siyasa ce a matakin ƙasa, wacce ke fafutukar kawo haɗin kai a mulki da kuma ƙarfafa matasa da mata su shiga siyasa.