Kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana bakwai ta mayar da kuɗaɗen ma’aikata da ake zargin an karkatar daga Asusun Tallafin Inshora na Ƙasa (NSITF), tare da gaggauta kafa Hukumar Gudanarwa ta Hukumar Fansho ta Ƙasa (PENCOM).
A cikin sanarwar da ta fitar bayan taron Kwamitin zartarwa a Abuja, ranar Laraba, NLC tayi gargadin cewa rashin cika waɗannan buƙatu zai haifar da yajin aikin ƙasa baki ɗaya.
Taron, ƙarƙashin jagorancin Shugaban NLC, Ƙwamared Joe Ajaero, ya tattauna matsalolin da ke shafar ma’aikatan Najeriya, ƙungiyoyin ƙwadago, da halin da ƙasar ke ciki.
Kwamitin ya zargi gwamnati da watsi da jin daɗin ma’aikata da kuma lalata tsarin gudanar da fansho, inda NLC tace dole ne a binciki batun karkatar da kuɗaɗen ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma, NLC ta sanar da rushe shugabancin ƙungiyar a jihar Edo ba tare da bayyana dalili ba.