Kotun ta tura wata mata gidan yari kan zargin ta da yiwa wasu ƴan mata tsafi a Kano 

0
13

Kotun Majistiri mai lamba 7 da ke Nomansland, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Halima Wali, ta tura wata mata mai suna Fauziyya Abubakar gidan yari bisa zargin ta da shiga wani gida a unguwar Lamido Crescent,  birnin Kano domin yin fitsari, inda daga aka gano cewa ta watsa wani magani a gidan, da ya jefa ƴan matan gidan cikin halin rashin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa, matar gidan, Malama Bilkisu, ta bayyana cewa ƴaƴan ta biyu da kuma ƴar maƙociyar ta sun kamu da ciwo mai ban mamaki, inda ɗaya jikinta ya fara tsatstsagewa, ɗaya kuma idan an yi mata kitso sai kanta ya warware kitson, yayin da ɗayar ta fara yin kukan kare.

An kuma zargi Fauziyya da ɗaukar auduguar mata da ta gani a bandakin gidan.

A zaman kotun, Mai shari’a Halima Wali, ta ƙi bayar da belin wacce ake zargi, saboda tsananin halin da yaran ke ciki, tare da sanya ranar 15 ga Satumba 2025 domin ci gaba da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here