Har Yanzu Ba a Ba Mu Dalar Amurka 100,000 da Tinubu Ya Yi Mana Alƙawari ba

0
39

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta bayyana cewa har yanzu ba su samu kuɗin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari ba bayan sun lashe gasar WAFCON a Maroko.

Ajibade ta ce jinkirin biyan kuɗin yana da ban takaici, duk da cewa ita ce ta jagoranci tawagar da ta sake lashe kofin WAFCON a bana.

Bayan nasarar, Shugaba Bola Tinubu ya ba su lambar yabo ta ƙasa (OON), tare da alƙawarin bai wa kowanne ɗan wasa dalar Amurka 100,000 da gida mai ɗaki uku a Abuja.

Lokacin da ya tarbe su a fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya yaba da jajircewarsu yana mai cewa nasararsu ta ɗaga martabar Najeriya a idon duniya.

Sai dai ƴan wasan sun ce har yanzu babu abinda aka basu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here