Gwamnatin tarayya zata kashe Naira biliyan 493 a ayyukan raya kasa a Kano da Lagos

0
11

Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da kashe N493bn domin manyan ayyuka biyu na gyaran hanyar Kano zuwa Katsina mai tsawon kilomita 152 da kuma gina sabuwar gada a jihar Legas.

Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ne ya bayyana haka bayan taron majalisar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Laraba.

Umahi ya ce hanyar Kano Katsina za a raba aikin zuwa sassa biyu:

Sashi na farko mai tsawon kilomita 74.1, wanda aka fara bayar da kwangilarsa tun 2013 akan biliyan 14, daga baya aka ƙara zuwa biliyan 24bn, yanzu kuma kudin ya kai biliyan 68.

Sashi na biyu kuma mai tsawon kilomita 79.5, an bayar da kwangilarsa a 2019 akan Naira biliyan 29, daga baya aka ƙara zuwa Naira 46, yanzu kuma ya kai Naira biliyan 66.115.

Game da sabuwar gadar da za’a yi a Lagos kuwa, Umahi ya bayyana cewa aikin zai laƙume Naira biliyan 359.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here