Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da cewa zai tafi hutun mako uku domin kula da lafiyarsa.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar, an bayyana cewa hutun zai fara daga Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.
Gwamna Radda ya ce domin tabbatar da lafiyata da kuma yin aiki cikin ƙwazo da yanayi mai kyau, na yanke shawarar tafiya wannan hutu. Zan dawo aiki da zarar likitoci sun kammala duba lafiyata.”
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa gwamnan ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, har zuwa lokacin da zai kammala hutun.
A watan Yuli da ya gabata, Gwamna Radda ya gamu da haɗarin mota a kan hanyar Katsina zuwa Daura.