Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce a cikin watanni takwas da suka gabata ta kashe ’yan ta’adda 592 tare da lalata kayayyakin aikin su 372 a hare-haren sama da ta kai a Jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce hare-haren wanda suka haɗa tashin jiragen yaƙi sau 798 sun rage ƙarfin ISWAP da Boko Haram sosai.
Babban Hafsan Sojin Saman, Air Marshal Hasan Abubakar, ya ce an lalata motocin ’yan ta’adda 206 da wuraren haɗa abubuwan fashewa 166, tare da ci gaba da kai hare-hare dare da rana daga Gonori zuwa Mallam Fatori.
Abubakar ya yaba wa gwamnatin Borno kan dabarun haɗin gwiwa da al’umma, yayin da Gwamna Babagana Zulum ya yi kira da a ƙara matsa ƙaimi wajen fatattakar ’yan ta’addan.