Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen jihar Kano ta kama mutum 49 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a ranar 7 da 8 ga watan Agusta.
An kama mutum 34 a Massallacin Idi, Fagge Plaza, Kofar Mata, Kofar Wambai, Kofar Dan’agundi, Ladanai, Zage da Tashar Rimi. Haka kuma an kama mutum 15 a Tashar Mota ta Kano Line da Na’ibawa.
Hukumar ta kwace tabar wiwi, codeine, diazepam, Pregabalin, Rohypnol, “suck and die”, sinadarin “Sholisho” da makamai.
Kwamandan NDLEA a Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya ce za su ci gaba da rushe cibiyoyin safarar ƙwayoyi tare da gurfanar da wadanda ake zargi a kotu.
Ya gargadi masu hannu a shaye-shaye da su daina, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen sauke nauyin dake kanta.