Jam’iyyun siyasa sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya a yayin zaɓukan cike gurbi na Kano

0
56

Jam’iyyun siyasa a jihar Kano sun sha alwashin kiyaye zaman lafiya a gabanin zaɓukan cike gurbi da aka shirin gudanarwa ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025.

Wannan alƙawari ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta shirya a ranar Talata a hedikwatar ‘yan sanda ta jihar.

Taron ya haɗa ‘yan takara da shugabannin jam’iyyu daban-daban da ke fafatawa a zaɓen na mazabar Ghari/Tsanyawa da na cike gurbi na mazabar Bagwai/Shanono.

 A yayin taron, dukkan mahalarta sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, inda suka amince da gudanar da harkokin zaɓe cikin lumana da bin doka kafin, yayin, da bayan zaɓen.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Dr. Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga dukkan jam’iyyu su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya, tare da gargadin cewa duk wanda ya aikata take doka zai gamu da daukar mataki. Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa an tanadi isassun jami’an tsaro domin kare masu kada kuri’a, ‘yan takara, da jami’an jam’iyyu a duk tsawon lokacin zaɓen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here