Gwamnatin Tarayya ta sanya takunkumin shekaru bakwai na dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi na tarayya, saboda yawaitar makarantu da ake da su amma ba a cikakken amfani da su ba, ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa, da kuma raguwar ingancin ilimi.
Wannan matakin ya samu amincewar majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da ta yi ranar Laraba a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, bayan gabatarwar da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa ya yi.