Ƴan Sanda Sun Kama Ɗaurarru Bakwai da Suka Tsere daga Gidan Yari na Keffi

0
11

Hukumar Kula da Gidajen gyaran hali ta ƙasa ta tabbatar da kama mutum bakwai daga cikin ɗaurarru 16 da suka tsere daga gidan yarin Keffi, Jihar Nasarawa.

A wata sanarwa da aka fitar a jiya Talata, hukumar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiya, lokacin da wasu daga cikin ɗaurarrun suka yi wa jami’an tsaro kutsa, lamarin da ya bai wa mutum 16 damar tserewa.

Mai magana da yawun hukumar, Umar Abubakar, ya ce jami’an tsaro biyar sun ji raunuka, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali kuma suna jinya a asibiti.

Hukumar ta ce an tsaurara matakan tsaro tare da kaddamar da bincike kan faruwar lamarin, karkashin jagorancin Babban Kwanturolan hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here