Hukumar Kula da albarkatun Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an samu raguwar yawan amfani da man fetur a watan Yuni 2025, inda jimillar man da aka fitar ya sauka zuwa lita biliyan 1.44.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na NMDPRA, George Ene-Ita, ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba, bisa rahoton cewa matsakaicin yawan amfani da mai a kowace rana ya kai lita miliyan 48.
Ene-Ita ya ce jimillar man da aka fitar a watan Yuni shi ne lita 1,440,768,129, wanda hakan ke nuna raguwa da kashi 16.42% idan aka kwatanta da watan Mayu da aka fitar da lita biliyan 1.768, wato sama da lita miliyan 290 ne suka ragu.
NMDPRA ta ce wannan raguwa na nuna cewa har yanzu ana fuskantar ƙalubale a harkar samarwa da rarraba man fetur a Najeriya, amma ta yi alkawarin yin aiki tare da masu ruwa da tsaki don tabbatar da isasshen rarrabawa da wadatar mai a faɗin ƙasa.