Hukumar hana fasa ƙauri ta ƙasa ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai, miyagun ƙwayoyi, magungunan da wa’adinsu ya ƙare, da sauran haramtattun kaya a tashar jiragen ruwa ta Apapa, Jihar Legas, a ranar Litinin.
A cewar Hukumar, an kama mutane shida da ake zargi da hannu a cikin safarar waɗannan kaya zuwa Najeriya ta hanyar fasa-ƙauri.
Shugaban hukumar , Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa an yi ƙarya wajen bayyana nau’in kayan da kwantainonin ke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista.
“Muna sanar da kama kwantainoni 16 waɗanda shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya kan waɗannan kaya ya haura Naira biliyan 10,” in ji shi.