Gwamnatin Kano ta rabawa ma’aikatu babura da motocin aiki

0
19

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya raba sabbin motoci 20 da babura 25 ga ma’aikatun gwamnati domin inganta ayyuka da ci gaban jihar.

An gudanar da rabon ne a fadar gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin, inda Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan, Dr. Sulaiman Wali Sani (mni), ya wakilci gwamna yayin rabon.

Gwamnan ya bukaci wadanda suka amfana da su kula da kayan yadda ya kamata, yana mai cewa wannan mataki na daga cikin kudirin gwamnatinsa na karfafa isar da ayyuka ga jama’a.

Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Malam Mustapha Muhammad, ya ce za a ci gaba da raba karin motocin ga sauran ma’aikatu har sai an kammala. Ya kara da cewa wannan shiri zai taimaka wajen kai wa jama’a alherin dimokuradiyya kai tsaye tare da karfafa aiki a hukumomin gwamnati.

Shugaban Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, Abba El Mustapha, wanda ya yi jawabi a madadin wadanda suka amfana, ya gode wa gwamnan tare da alkawarin amfani da motocin wajen tallafa wa shirye-shiryen ci gaban jihar.

Cikin wadanda suka amfana akwai Ma’aikatar Ma’adinai da Albarkatun Ƙasa, Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire, Hukumar Inganta Ƙananan Sana’o’i, Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, Hukumar dakunan karatu ta Jihar Kano, Ma’aikatar Tsaro, Hukumar Tsara Birane, Rediyon Jihar Kano, Hukumar Kididdiga, Hukumar Kananan Sana’o’i da Tallace-Tallace a Kan Titi, Sashen Motar Asibitin Fadar Gwamnati, da Asibitin Nuhu Bamalli, inda Rundunar Hisbah ta samu babura 15.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here