Gwamnan Kano ya samu yabo akan biyan fansho

0
17

A Najeriya, yawancin tsoffin ma’aikata na fama da ƙarancin kuɗin fansho da jinkirin biyan su, wanda ya kai biliyoyin naira a bashin jihohi da dama. 

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano yayi fice a wannan fanni saboda jajircewarsa wajen rage wannan bashi, inda ya raba sama da ₦ 22bn tun daga 2023 domin biyan fansho da gratuity.

A cikin shekara biyu na farko, ya biya rabin bashin kuma ana sa ran zai gama kafin ƙarshen wa’adinsa. 

Masana sun ce idan sauran gwamnoni suka yi koyi da shi, za a rage cin hanci da kare ma’aikata daga wahalar fansho a nan gaba.

Tonnie Iredia, wanda Farfesa ne a fannin aikin jarida, kuma tsohon shugaban talabijin ta kasa NTA, shine ya bayyana hakan cikin wani saƙon daya wallafa, ya kuma soki kuɗaɗen alfarma da ke kashewa kansu da kansu.

Ya kuma ja hankalin gwamanti data daina jiran zanga-zangar tsoffin jami’an tsaro kafin a biya su hakkinsu, domin hakan na iya zama barazana ga zaman lafiya da mutuncin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here