Fiye da mutane Miliyan 1.9 Sun Nemi Aikin Hukumomin Gwamnatin tarayya 

0
12

Fiye da ‘yan Najeriya 1,911,141 ne suka nemi aikin Hukumomin tsaron a’lumma ta farin kaya, kula da shige da fice, kashe gobara, da jami’an kula da gidajen gyaran hali, (CDCFIB) kafin kammala karɓar takardun neman aikin a ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa aikin daukar ma’aikatan ya gamu da tangarɗa, wanda yasa sau da dama shafukan yanar gizon hukumar daina aiki, tare da dakatar da tsarin na wucin gadi.

Asalin jadawalin fara karɓar takardun masu neman aikin shi ne ranar 26 ga Yuni, amma an dage shi zuwa 14 ga Yuli, daga bisani aka sake dagewa zuwa 21 ga Yuli. Saboda haka, lokacin rufe neman aikin da ake sa ran zai kasance ranar 4 ga Agusta, an ƙara mako guda, ya koma ranar 11 ga Agusta.

Duk da wannan jinkiri da cikas, alkaluman hukumar sun nuna cewa sama da mutane miliyan 1.9 sun mika bukatar neman aikin.

Jihohin da suka fi yawan masu nema sun haɗa da Kogi (116,162), Kaduna (114,536), da Benue (110,565), yayin da Bayelsa (11,669) da Lagos (14,216) suka fi ƙarancin masu nema.

Jimillar mutane 510,174 daga jihohin Kogi, Kaduna, Benue, Kano da Niger ne suka fi rinjaye a jerin masu nema, yayin da jihohin Bayelsa, Lagos, Rivers, Ebonyi da Delta suka samar da jimillar masu nema 99,658.

Hukumar ta shawarci masu neman aikin da su ci gaba da bibiyar sakonnin shafin aikewa da sako na Email da na waya, tare da duba shafin yanar gizo da shafukan sada zumunta na CDCFIB don samun sabbin bayanai a makonni masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here