Bankin Duniya ya amince da kasafin kuɗi na dala miliyan 300 domin aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar ’yan gudun hijira a arewacin Najeriya.
A cewar sanarwar da jaridar Daily Trust ta ruwaito, wannan shiri mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project (SOLID), wanda aka amince da shi ranar 7 ga Agusta, zai samar da hanyoyin taimako ga ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suke zaune tare da su.
Bankin ya bayyana cewa rikice-rikicen da suka daɗe suna addabar yankin sun raba fiye da mutum miliyan 3.5 da muhallansu, abin da ya haifar da ƙarancin ababen more rayuwa a garuruwan da suke rayuwa yanzu.
Shirin zai mayar da hankali kan:
Rage illolin sauyin yanayi
Samar da haɗin kai da zaman lafiya
Tallafa wa iyalai
Inganta ababen more rayuwa
“Muna matuƙar farin cikin ƙaddamar da wannan aikin domin taimaka wa Najeriya wajen shawo kan matsalolin da take fuskanta,” in ji Mathew Verghis, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya.