Atiku Ya Zargi Tinubu da Yin Amfani da EFCC Wajen Tsorata ’Yan Adawa

0
7

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kamawa ada tsare tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da Hukumar EFCC ta yi, na da alaƙa da shigar Tambuwal cikin haɗakar jam’iyyun hamayya.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da yaƙi da cin hanci a matsayin makamin murƙushe ’yan adawa da tilasta musu shiga jam’iyya mai mulki.

Ya ce, wannan ba shi ne manufar kafa hukumar EFCC ba, yana mai cewa duk wani ɗan siyasa da yake cikin adawa yanzu yana fuskantar barazanar tuhumar rashawa, amma idan ya koma jam’iyya mai mulki sai a yi masa afuwa.

Atiku ya jaddada cewa yaƙi da cin hanci lamari ne da ya kamata a mara masa baya, amma haɗa shi da manufofin siyasa abu ne mara kyau.

A ƙarshe, Atiku ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ba za su yi shiru suna kallo ana lalata dimokuraɗiyya ta hanyar mayar da ƙasa karkashin mulkin jam’iyya ɗaya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here