Wasu mayakan Boko Haram sun kashe sojoji da dama tare da yin garkuwa da wata ɗaliba a wani mummunan hari da suka kai a daren Asabar a garin Kukawa, ƙaramar hukumar Gwoza, a jihar Borno, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin tserewa domin tsira da rayukansu.
Shaidu sun ce harin ya fara da misalin ƙarfe 9:30 na dare, inda ‘yan ta’addan suka ƙona gidaje, shaguna da motocin jama’a, yayin da suke musayar wuta mai tsanani da dakarun Multi JTF.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, da dama daga cikin mazaunan yankin sun tsere zuwa ƙasar Kamaru domin gujewa tashin hankali.
Majiyoyi sun bayyana cewa, wata ɗaliba mai suna Aisha Muhammad ce aka sace a harin, har yanzu kuma ba a sako ta ba.
Rundunar ‘yan sanda ta ce har yanzu tana ci gaba da tattara cikakken bayanai kan yawan asarar da aka yi a harin.