Wata motar haya ɗauke da magoya bayan jam’iyyar APC ta yi hatsari a ƙauyen Yakasawa, ƙaramar hukumar Ringim, jihar Jigawa, inda mutane 18 suka ji rauni, a ranar Lahadi.
Lamarin ya faru ne kusan kilomita biyu daga garin Ringim, inda jama’a suka taru domin tarbar Gwamna Umar Namadi a bikin shirin haɗin kai tsakanin gwamnati da jama’a na karo na 15.
Shaidu sun bayyana cewa motar Volkswagen Golf mai lambar FKJ 102 JB tana gudu sosai, kafin direban ta ya yi ƙoƙarin kauce wa rami akan hanya, inda ya afka cikin taron mutane.
Jami’an NSCDC da FRSC sun garzaya da waɗanda abin ya rutsa da su zuwa Asibitin Gwamnati na Ringim. Ba a samu asarar rai ba, sai dai wasu sun samu raunuka masu tsanani.
Mai magana da yawun NSCDC, ASC Badruddeen Tijjani, ya ce an fara bincike kan lamarin, tare da kira ga direbobi su rika tuki a hankali musamman a wuraren da ake da ramuka a hanya.