Gwamnatin Katsina ta mayar da martani kan rahoton MSF kan mace-macen yara

0
24

Gwamnatin Jihar Katsina ta yi karin bayani kan rahoton da ƙungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar, wanda ya bayyana cewa aƙalla kananan yara 652 ne suka rasu cikin watanni shida a jihar sakamakon ƙarancin abinci mai gina jiki.

A rahoton da MSF ta fitar a ƙarshen mako, ƙungiyar ta ce raguwar tallafin kuɗaɗe daga ƙasashen waje na kawo cikas ga ayyukanta, musamman a ƙasashe masu tasowa. Barista Bulama Bukarti ya bayyana cewa, a cikin watanni shida na farko na wannan shekarar, MSF ta karɓi aƙalla yara 70,000 a asibitocinta, inda fiye da 10,000 aka kwantar, da su daga ciki kuma yara 652 suka rasu a Katsina.

A martanin gwamnatin jihar, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko, Dr. Shamsuddeen Yahaya, ya ce akwai matsalar tamowa a Katsina kamar yadda take a sauran jihohin arewa maso yamma, amma akwai kuma wasu ƙalubale da ke tsananta lamarin. Ya ce gwamnatin Katsina ta ƙara ware naira miliyan 500, a kan naira miliyan 500 da aka ware tun farko, domin yaki da matsalar yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki.

Gwamnatin ta ƙara ƙarfi da cewa akwai wasu cututtukan dake kashe yara, ba yunwa kaɗai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here