Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da bikin yaye sama da matasa 500 da suka tuba daga harkar Daba a karkashin shirin Safe Corridor Project.
Bikin ya gudana a Ma’aikatar Sufuri, inda Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, a wajen taron.
An bayyana cewa shirin an samar da shi don bawa matasa damar rungumar zaman lafiya, samun ilimi, da shiga ayyukan gwamnati.
Haka kuma hukumar NDLEA za ta bawa masu shaye-shaye magani, yayin da wasu za a mayar makaranta.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa matasan bisa ajiye makamansu, yana mai cewa gwamnatin Kano ta dauki mataki mai kyau wajen magance matsalar Daba da shaye-shaye a jihar.