Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, yana tsare a ofishin Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) a Abuja, inda ake yi masa tambayoyi kan zargin cire kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba har Naira biliyan 189.
Rahotanni sun nuna cewa, waɗannan kuɗaɗen an cire su ne cikin sabawa dokar hana fitar kuɗaɗen haram ta shekarar 2022. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da lokacin da aka yi waɗannan cire-cire ba.
Majiyar cikin gida ta EFCC ta bayyana cewa tsohon gwamnan ya isa babban ofishin hukumar da misalin ƙarfe 11:30 na safe, inda ya fara fuskantar tambayoyi.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ƙi yin wani bayani game da lamarin lokacin da aka tuntube shi.