An gudanar da sallar jana’izar ‘yan jaridar Al Jazeera guda biyar da suka rasu sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza a daren Lahadi.
Rahoton Al Jazeera ya ce an fitar da gawarwakin daga asibitin al-Shifa, inda aka kashe su, zuwa gidajensu domin yi musu sutura.
Hotunan da suka fito daga Gaza sun nuna yadda dubban jama’a suka halarci jana’izar cikin alhini da jimami.
Hare-haren Isra’ila sun hallaka shahararren ɗan jarida Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa huɗu a wani hari da aka kai arewacin Gaza. Isra’ila ta ce tana zargin al-Sharif da alaƙa da Hamas, tana mai cewa ta kashe shi ne saboda rahotanninsa masu tsanani daga yankin.
Sauran ‘yan jaridar da suka rasu su ne Ibrahim Zaher, Mohammed Noufal, da Moamen Aliwa, dukkaninsu ma’aikatan Al Jazeera.