Amurka Ta Yi Allah-wadai da Kisan Kiristoci a Najeriya

0
60

Gwamnatin Amurka ta yi Allah-wadai da hare-haren da tace ana kai wa Kiristoci a Najeriya da sauran kasashen Afrika, tana mai kiran lamarin mummunan zalunci da kuma alƙawarin yin aiki da ƙasashen duniya don shawo kansa.

A baya-bayan nan, mace wasu mahara sun kashe Kiristoci 27 a ƙauyen Bindi Ta-hoss, jihar Filato, inda da dama aka ƙone  su da ransu a coci. Haka kuma, a ranar 27 ga Yuli, an kashe Kiristoci 49 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta hannun mayakan ADF masu alaka da ISIS.

Kungiyoyin Boko Haram da ISWAP na daga cikin masu kai hare-hare da kisan gilla, da sauran su.

Jaridar Guardian tara a shekaru goma, an kashe sama da mutum 150,000, an kuma kori Kiristoci miliyan 16 daga gidajensu, a Najeriya.

Shugabannin addini da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce wannan wani yunkuri ne na “kisan kare dangi ne” da ake yi ba tare da ɗaukar mataki mai karfi ba.

Sai dai abin dubawa shine wannan rashin tsaro a Najeriya ya shafi mabiya kowane irin addini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here