Zan kawar da cin hanci a watan farko ko nayi murabus–Ameachi

0
7

Tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce idan ya zama shugaban ƙasa a 2027 ƙarƙashin jam’iyyar ADC, zai kawar da cin hanci da rashawa cikin watan farko na mulkinsa, ko ya yi murabus.

Amaechi ya zargi gwamnatin yanzu da karkatar da ribar cire tallafin man fetur zuwa aljihun ‘yan kaɗan daga cikin jami’an gwamnati da gwamnoni, yana mai cewa shi zai sa ido domin kuɗin su koma hannun jama’a don ragewa ƴan ƙasa talauci.

Ya kuma ce ba zai dawo da tallafin man fetur ba, amma zai tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka tattara daga cire tallafin za su inganta tattalin arzikin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here