Mahara sun kashe mutum biyu, da  ƙona gidaje a Jihar Filato

0
12

Wasu mahara sun afka wa Karamar Hukumar Bokkos, ta Jihar Filato, inda suka kashe mutum biyu tare da ƙona gidaje da coci-coci a daren Lahadi.

Shugaban ƙungiyar ci gaban al’ummar Bokkos, Farmasun Fudang, ya bayyana cewa waɗanda suka mutu ma’aikata ne a wata coci, kuma an ƙona gidaje da dama da wuraren ibada. Ya ce maharan sun kuma lalata gonaki, sun yi awon gaba da shanu, tumaki, awaki, agwagi da sauran su.

Fudang ya bayyana cewa maharan sun shigo ne ta hanyar Ding’ak da Kopmur duk da kasancewar akwai shingen jami’an tsaro a wajen. A cewarsa, sojoji sun yi harbi a iska amma ba su yi musayar wuta da maharan ba.

Harin ya faru kwanaki biyu bayan makamancin sa a yankin Ndimar. Shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar su kawo ɗaukin gaggawa tare da tabbatar da hukunta masu aikata irin waɗannan laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here