Haɗakar jam’iyyu ce kaɗai hanyar kifar da gwamnatin Tinubu—Shekarau

0
11

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa haɗin kan jam’iyyun siyasa ce hanyar kifar da gwamnatin Tinubu, a 2027, ba wai ɗaiɗaikun ƴan takara ba.

Ya shawarci jam’iyyun adawa su manta da son rai, su haɗa kai wajen kafa ƙawance mai ƙarfi da zai iya kalubalantar jam’iyya mai mulki.

Shekarau ya tunatar da al’umma yunƙurin da aka yi a 2011 na haɗa ACN, CPC da ANPP domin hambarar da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, amma shirin ya gaza sakamakon kowane ɗan takara ya tsaya da jam’iyyarsa.

Ya ce ya kasance cikin manyan masu ruwa da tsaki a wancan yunƙuri, inda suka yi taruka da dama har a gidajen Tinubu da Buhari, amma tattaunawar ta rushe kafin cimma matsaya.

Shekarau ya bayyana cewa darussan da aka koya daga gazawar 2011 ne suka jagoranci nasarar haɗuwar CPC, ACN da ANPP a 2015, lokacin da kowace jam’iyya ta shiga tattaunawa a matsayin ƙungiya ba mutum ɗaya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here