Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Na Ƙasa Audu Ogbeh, Ya Rasu

0
18

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa kuma tsohon Ministan Noma daga shekarar 2015 zuwa 2019), Cif Audu Ogbeh, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya.

Rahotonni sun bayyana cewa ya rasu a yau Asabar, 9 ga watan Agusta.

A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun ce za a sanar da cikakken jadawalin jana’izarsa a nan gaba. Sun kuma gode wa abokai, abokan aiki da masoya bisa addu’o’i da alhini da suke nunawa a wannan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here