Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da korar wasu manyan hadiman sa biyu saboda laifukan da suka shafi rashin kyawawan halaye.
Sanarwar hakan ta fito daga bakin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, inda ya bayyana cewa korar ta shafi Abubakar Umar Sharada, Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman kan Huldar Siyasa, da kuma Tasiu Adamu Al’amin Roba, Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman a Ofishin Majalisar Zartarwa.
Wani rahoton kwamitin bincike ya gano Sharada da hannu wajen ba da beli ga wani da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. An umurce shi da ya mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunsa zuwa ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, tare da gargadin kada ya sake gabatar da kansa a matsayin jami’in gwamnati.
Roba kuwa, an tsige shi daga mukaminsa bayan samun sa da hannu a cikin zargin aikata ba daidai ba a rarraba kayan tallafin gwamnati a wata ma’ajiya da ke Sharada a 2024. Yanzu haka yana fuskantar shari’a kan zargin sata da kuma hada baki wajen aikata laifi. Shi ma an umurce shi da ya mika kayan gwamnati dake wajen sa, kafin ranar 11 ga Agusta.
Sai dai kuma, kwamitin bincike ya tabbatar da cewa Hon. Musa Ado Tsamiya, Mai Baiwa Gwamna Shawara kan Magudanan Ruwa, bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba, lamarin da ya sa aka wanke shi gaba daya.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashawa ko rashin da’a ba, tare da jan hankalin jami’an gwamnati da su kiyaye halin kirki da nagarta a ayyukansu.