Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tarbi manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga karamar hukumar Dawakin Tofa da suka sauya sheka zuwa NNPP tare da dimbin magoya baya.
Taron tarbar ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin mai magana da yawun gwamnan, DG Sanusi Bature D-Tofa, tare da shugaban karamar hukumar, Hon. Alhaji Anas Mukhtar Bello Danmaliki, inda ya samu halartar fitattun jiga-jigan NNPP.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ci gaba da maraba da duk wanda yake da kishin kawo canji mai ma’ana da ci gaban al’umma a kowacce jam’iyyar siyasa yake domin shigowa NNPP.