Babu gaskiya a rahoton cewa bamu samu masu zuba jari a Kano ba—Gwamnati

0
13
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta karyata rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) da ya nuna jihar ta samu dala dubu 120 kacal na jarin kasashen waje a farkon zangon shekarar 2025.

Darakta Janar na Hukumar Kula da Masu Zuba Jarin Waje ta Kano (Kan-Invest), Muhammad Nazir Halliru, ya ce adadin da NBS ta fitar ba gaskiya ba ne, domin a zahiri jihar ta samu fiye da dala miliyan 22 daga hannun jarin kasashen waje a fannoni kamar makamashi da shirye-shiryen iskar gas (CNG da LNG). Ya ce NBS ta wallafa rahoton ne ba tare da ta tuntuɓi gwamnati ko samun sahihin bayani daga jihar ba.

Ya ƙara da cewa akwai wasu manyan hannun jarin da ke kan hanya, tare da burin jihar na tara dala biliyan 10 cikin shekaru biyar masu zuwa. Gwamnatin Abba Kabir Yusuf, in ji shi, na da ƙuduri na ƙarfafa jarin da ake da shi da kuma jawo sababbi don bunƙasa tattalin arzikin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here