An ɗaura auren fitacciyar jarumar fina-finan Najeriya, Rahma Sadau, da Alhaji Ibrahim Garba a ranar Asabar a Kaduna.
An gudanar da ɗaurin auren ne misalin ƙarfe 11 na safe a Masallacin Atiku Auwal da ke Unguwar Rimi, inda ‘yan uwa da abokan arziki kaɗan suka halarci taron.
An bayyana Naira dubu ɗari 3 a matsayin sadakin aurenta.
Majiyoyi sun ce jarumar ta zaɓi yin bikin a sirrance.