Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince a mayar da gidan marayu na Gaya zuwa cibiyar gyaran halin mata masu fama da matsalar shan miyagun ƙwayoyi.
Matakin na daga cikin jerin sabbin ayyukan gwamnati da suka kai kimanin naira biliyan 14.8, da nufin inganta ci gaban jihar baki ɗaya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, bayan zaman majalisar karo na 30 da aka gudanar a ranar Laraba, 6 ga Agusta.
A cewar bayanin, Ma’aikatar Ayyuka ta samu kaso mafi tsoka na kuɗin, naira biliyan 11.8, wanda za’a yi amfani dashi wajen sauya gidan marayu zuwa cibiyar gyaran halin mata a Gaya, gina cibiyar masaukin gaggawa a ƙaramar hukumar Gaya, sake ba da kwangilar gina hanyar Jaba–Gayawa, da shimfiɗa hanyar Dakata–Yadakunya (Bela) zuwa titin Badgery–Yusuf Road a ƙaramar hukumar Nassarawa.
Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Gine-gine ta samu naira miliyan 882.9 don ɗab’in takardun tsaro da faɗaɗa wasu ayyuka, yayin da Ma’aikatar Lafiya ta samu naira biliyan 1.66 domin gyaran asibitoci, sanya na’urorin hasken rana a cibiyoyin haihuwa, samar da magunguna da kuma inganta cibiyoyin lafiya a matakin farko.
A ɓangaren ruwa, an amince da naira miliyan 310 don samar da man fetur, sai kuma naira miliyan 169.6 da aka ware ga Ma’aikatar Ci gaban Karkara da Al’umma domin gyaran ƙananan dam guda biyar a Madobi, Gwarzo, Garun Malam, Kibiya da Ajingi.
Majalisar ta kuma amince da ƙarin kasafin kuɗi na 2025, da ya kai naira biliyan 889.27, wanda ya ƙaru da sama da naira biliyan 169.5 fiye da asalin kasafin, wanda za’a tura wannan buƙata zuwa Majalisar Dokoki ta Jihar Kano domin amincewa.