Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ɗauki nauyin karatun dalibai mata uku daga jihar Yobe, wadanda suka lashe manyan kyautuka a gasar TeenEagle Global Finals, a birnin Landan na ƙasar Burtaniya.
A cikin wata wasiƙa da aka rubuta a ranar 5 ga Agusta, 2025, wacce Sakataren Gidauniyar Atiku Abubakar, Farfesa Ahmadu Shehu ya sanyawa hannu, an taya ɗaliban, Nafisa Abdullahi, Rukaiya Mohammed Fem, da Khadija Kashim Kalli, murna bisa abin da gidauniyar ta bayyana a matsayin “gagarumar nasara.” da suka masu da gasar TeenEagle.
Wasiƙar ta bayyana cewa gidauniyar za ta ɗauki nauyin cigaban karatunsu na sakandare da kuma karatun jami’a a kowace jami’ar da suka zaɓa.