Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bai wa iyalan ‘yan wasan Kano 22 da suka mutu a haɗarin mota tallafi na naira miliyan 110, inda kowane iyali ya samu naira miliyan 5.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shima ya bada gudummawar naira miliyan 130 da filaye.
Tuni gwamnatin Kano ta bayar da tallafin farko na naira miliyan 22 tun bayan haɗarin.
Jimillar tallafin da aka tattara ya kai naira miliyan 321.2 tare da buhuna 30 na shinkafa da filaye.