Sojin Sama sun kai hari wajen bikin auren ‘yan bindiga a Zamfara

0
9
jiragen yaki

Rundunar Sojin Sama ta kai hari ta jirgin yaki kan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka taru domin bikin aure a tsaunukan Asaula da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa harin, wanda aka kai da misalin karfe 4 na yamma ranar Talata, ya kashe ‘yan bindiga da dama, inda wasu kuma suka jikkata sosai. Akalla gawa 10 aka gano, yayin da wasu suka kone har ba a gane su.

Wasu daga cikin wadanda suka jikkata, kimanin 33, na karbar magani a cibiyar lafiya ta Yankuzo da wasu kauyuka.

Wannan hari na cikin shirin Operation Fansar Yan Bindiga da gwamnatin tarayya ta kaddamar don yakar ta’addanci a jihohin Zamfara, Katsina, Kebbi da Sokoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here