Shugaba Tinubu ya nada Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar NERC

0
7

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa (NERC), kuma zai rike wannan mukami a matsayin mukaddashi har sai majalisar dattawa ta tabbatar da nadin nasa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis.

Injiniya Ramat, wanda ya taba zama shugaban ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano daga 2021 zuwa 2024, yana da digiri na uku (PhD) a fannin Gudanar da Dabaru, tare da ƙwarewa a fannin Injiniyan wutar lantarki da shugabanci.

Baya ga wannan, Shugaba Tinubu ya kuma naɗa Abubakar Yusuf a matsayin kwamishinan kula da harkokin masu amfani da wutar lantarki, da kuma Fouad Olayinka Animashun a matsayin kwamishinan harkokin kuɗi da gudanarwa a hukumar NERC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here