Bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a watan Oktoban 2024 tsakanin al’ummomi da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna da wasu ‘yan ta’adda da suka ce sun tuba, al’ummar yankin sun bayyana damuwa kan wata sabuwar barazanar rashin tsaro da ke tayar da hankali.
Yarjejeniyar zaman lafiyar ta biyo bayan kusan shekara goma na rikici da tashin hankali, wanda ya mai da hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi haɗari a Najeriya. Tun daga shekarar 2015.
Mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da sace-sace, inda matafiya ke shiga matsala.
Duk da haka, yankin ya fara samun ɗan sassaucin zaman lafiya, kuma yawancin mazauna da suka gudu sun fara komawa gidajensu tare da ci gaba da noma.
Sai dai al’ummar yankin sun ce, a yanzu maimakon sace mutane, ‘yan bindigar na yawo a gonaki da kauyuka suna kwace babura, wayoyi, kuɗaɗe, da kayan aikin manoma.
A wasu kauyuka kamar na Kuyello, mazauna sun ce sun koma zama cikin fargaba. Wasu ma sun daina zuwa gonakinsu gaba ɗaya, yayin da wasu ke barin wayoyinsu a gida domin kauce wa fashi.