Hukumar NDLEA ta Najeriya da hukumar NCB ta Indiya sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa domin yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu.
Shugabannin hukumomin biyu, Buba Marwa da Anurag Garg, sun bayyana hakan a wata ganawar da suka yi ta intanet, inda suka mayar da hankali kan hana shigowar ƙwayoyi kamar tramadol daga Indiya zuwa Najeriya.
Marwa ya bayyana cewa irin waɗannan ƙwayoyi suna da illa ga lafiya da tsaro, kuma ya nemi taimakon Indiya wajen bawa jami’an NDLEA horo na musamman don samun nasarar shirin.
Wannan matakin ya biyo bayan yarjejeniyar fahimta da aka cimma tsakanin kasashen a shekarar 2023, a ƙoƙarin Najeriya na magance safarar ƙwayoyi.