Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa ta kayyade kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 zuwa naira miliyan 8.5 a matsayin farashi na farko, kafin a kammala ƙididdiga da tattaunawa kan kuɗin ƙarshe.
Hukumar ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis, bayan wani taro da ta gudanar tare da shugabanni da sakatarorin hukumomin aikin Hajji na jihohin Najeriya, a wani bangare na shirye-shiryen aikin Hajjin baɗi.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana cewa wannan adadi na miliyan 8.5 ba shi ne kuɗin ƙarshe ba, illa dai an kayyade shi ne a matsayin “kafin alkalami” don fara tsare-tsaren ibadar Hajjin da ke tafe.
A cewarsa, gwamnatin Saudiyya ta sake ware wa Najeriya kujeru 95,000, kamar yadda ta yi a bara.