Masu ƙwacen waya sun kashe ɗalibin jami’ar Bayero Kano

0
12

Wani dalibi mai karatu a ajin shekara ta uku a Jami’ar Bayero Kano (BUK), Umar Abdullahi Hafizi, ya rasa ransa bayan da wasu da ake zargin masu satar waya ne suka caka masa wuka a unguwar Dorayi da ke karamar hukumar Gwale.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na dare, wanda ya girgiza al’ummar jami’ar, inda ɗalibai da ma’aikata ke bayyana alhini da jimami.

A wata sanarwa da jami’ar ta fitar, ta bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga jami’ar, duk da cewa lamarin bai faru a harabar makarantar ba. Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya tabbatar da cewa suna aiki tare da hukumomin tsaro don kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aiki.

An riga an kai gawar marigayin zuwa garinsu Zariya, jihar Kaduna, inda aka yi jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci. Jami’ar ta bukaci ɗalibai da su kwantar da hankalinsu tare da yin taka-tsantsan, sannan ta roƙi jama’a da su taimaka da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro.

BUK ta yi addu’a ga marigayin tare da roƙon Allah ya bawa iyalansa haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here