Fitaccen mai shirya bidiyon barkwanci a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello, ya rasa mahaifinsa.
Rahoton rasuwar ya fito ne a ranar Alhamis ta hannun abokinsa Barrister Abba Hikima, wanda ya wallafa sakon ta’aziyya a shafinsa na Facebook.
A cikin sakon da ya rubuta da Hausa, ya ce: “Innalillahi wa inna IlaiHi Rajiun. Allah ya yi wa Mahaifin Dr. Bello Galadanci (Dan Bello) rasuwa yanzun nan. Allah ya gafarta masa. Ameen.”