Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun shiga alhini sakamakon rasuwar mutum hudu ’yan gida ɗaya cikin wani mummunan al’amari da ba a san musabbabinsa ba.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka rasa rayukansu sun hada da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu da ’ya’yansu biyu Amos da Maryamu Yakubu.
Majiyoyi daga kauyen sun ce suna zargin hayakin da ya fito daga injin janareta da ake amfani da shi a gidan ne ya haifar da gubacewar iska, lamarin da ake ganin ya zama sanadin mutuwar tasu.
Ibrahim Samanja, wani ɗan uwan mamatan, ya ce ya gano rasuwar ne da safiyar Talata yayin da ya je gidan, sai ya lura da abin da bai saba gani ba. “Na zo da misalin ƙarfe 7:00 na safe, na dinga buga ƙofa ba wanda ya amsa. Hakan ne ya saka ni cikin damuwa, daga bisani na balle ƙofar, sai na iske su kwance babu rai,” in ji shi.
Bayan haka, ya sanar da jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya, inda suka je wurin da gaggawa kuma suka tabbatar da mutuwar su duka.
A halin yanzu, gawarwakin an kwashe su zuwa babban asibitin Marama domin ajiya da kuma gudanar da bincike kan abin da ya haifar da mutuwar.
Mazauna kauyen sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi kuma abin damuwa, inda suka ce kafin faruwar lamarin, mamatan ba su nuna wata alamar rashin lafiya ko wata matsala ba.
Sai dai binciken farko da aka gudanar ya nuna babu wata alamar tashin hankali ko wani mummunan abu da ya faru. Hakan ne ya jefa al’ummar yankin cikin zargin yiwuwar gubacewa ko shakar iska mai guba daga janaretan da suke amfani da shi.
Rundunar ’Yan Sandan jihar Borno ta bakin kakakinta, ASP Nahum Daso, ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa tuni an fara bincike domin gano musabbabin mutuwar.